ADDUO’IN MUMINAI VOLUME 2

ADDUO’IN MUMINAI VOLUME 2

Price Include Shipment
$55.00

Description

Adduo’in Muminai littafi na biyu (2) kamar littafi na (1) ya kunshi addu’oi masu yawa, masu dumbun albarka kuma littafi ne wanda yake dauke da adduo’i na chikin Alkur’ani Mai Girma, Mai Tsarki; adduo’i na chikin hadisan Annabin Rahama da kuma Sunayen ALLAH Masu Girma. ‫ىى‬Wannan littafi shima ya kunshi fiye da shafi dari biyar (500) na adduo’i Madaukaka Masu tasiri a kan al’amura masu yawa; kuma adduo’in sun fito ne daga chikin Al-kur’ani Mai Girma, Mai Tsarki da kuma chikin Hadisai na fiyayyen Halitta, shugaban Annabawa Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) wannan littafi shima yana da babi goma (10) kuma ko wane babi yana da adduo’i Madaukaka masu tasiri sosai akan al-amura na rayuwar duniya da lahira. ALLAH Ka sa albarka a wannan aikin da mukayi ka kuma amfanar da duk wanda yayi amfani da wadannan adduo’i naka don matsayin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ameen.